Saturday, April 4
Shadow

Cutar COVID-19: MOPPAN ta dakatar da shirya finafinai

SAKAMAKON ɓarkewar muguwar cutar nan ta ‘Coronavirus’, uwar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa, wato ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’ (MOPPAN), ta hana aikin shirya kowane irin fim a arewacin Nijeriya baki ɗaya.

 

Cutar, wadda a taƙaice ake kira ‘COVID-19’, ta na ta kashe bil’adama a yawancin ƙasashen duniya a yanzu, ciki har da Nijeriya.

 

Mujallar Fim ta ruwaito cewa gwamnatocin ƙasashe da na jihohi da sauran wuraren ayyuka da cuɗanya da juna sun bada umarnin cewa mutane su killace kan su kuma su ɗau matakan kariya don hana yaɗuwar cutar.

 

A cikin wata sanarwa da shugaban MOPPAN na ƙasa Dakta Ahmad Muhammad Sarari ya fitar a yau, kuma aka ba mujallar Fim, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin hana cigaba da yaɗuwar cutar.

 

Ta ce an hana duk wani aikin shirya fim har zuwa nan da kwana talatin.

 

Shugaban ya umarci dukkan ƙungiyoyin da ke cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood da su kulle duk wani wurin shirya fim inda ‘yan fim ke cuɗanya da juna, saboda a tsare rayuwar membobin su.

 

A sanarwar shugaban, wadda jami’in yaɗa labarai na MOPPAN na ƙasa Malam Al-Amin Ciroma ya rattaba wa hannu, ƙungiyar ta ce wannan mataki da ta ɗauka ya yi daidai da yunƙurin da Gwamnatin Tarayya da Cibiyar Yaƙar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) su ke wajen ganin daƙile yaɗuwar cutar.

 

Ta yi gargaɗin cewa duk wani ɗan fim da ya saɓa wa wannan umarni zai gamu da fushin hukuma, kuma ta sanar da jami’an tsaro wannan umarnin.

 

Haka kuma ta yi kira ga dukkan ‘yan fim da su ɗauki matakan kare kan su da aka bayyana tare da kula da lafiyar jikin su, kuma idan sun ji ba su gane yanayin lafiyar jikin su ba to su buga wa cibiyar NCDC waya ta lambar ta, wato 08097000010, ko su tura tes ga 08099555577; WhatsApp 07087110839 ko su tuntuɓe ta ta hanyar Facebook da Twitter da imel.

Fimmagazine

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *