Saturday, April 4
Shadow

SHUGABAN BUHARI YA YABAWA JIHOHI, HUKUMOMI, KAMFANONI, TSAYAYYUN KUNGIYOYI MASU GUDANAR DA AIKI, DAKE RAGE BARAZANAR KARANCIN ABINCI, DA MAGANI

Shugaban Kasa Muhammadu Bauhari ya yabi hadin kai da aka samu gurin yakan yaduwar Cutar Covid-19 a kasar, Musamman ta hanyar Killace kai, kaurace Cudanya, dakuma Gudumowa da Al’umma da Dai daikun Mutane da Hukumomi, Wanda suka taimaka ka’in da na’in da kudade don tabbatar da kokari Gwamnatin Tarayya da Jihohi.

 

 

Shugaban ya yaba wa Gwamnatochin jihohi, Jagorarin Addinai, Ma’aikatan Lafiya, Hukumomin Gwamnatin Tarayya, Ciki harda Jami’an tsaro, Hukumar kare Cutuka masu yaduwa ta kasa, National Centre for Disease Control (NCDC), Kungiyar masu sarafa kayan masaruhi na kasa, sakamakon kara kaimi don kare kasar da Al’umman ta, Ya bada tabbaci cewa Gwamnati zataci gaba da tsayawa kan Kafafunta don kara zuba Kudade don rage Nauyin Annobar.

 

 

Yayin daya kuma yi kira bin dokokin da aka shimfida na rage Tafiye tafiye da taron Al’umma don kiwon lafiyan dukkanin ‘yan kasar, Shugaban kasa Buhari yakuma kara tabbatar da cewa Umarni na Gwamnati bazai shafi Samar dakuma rarraba kayakin Masaruhi ba, Magunguna, kayakin jinya, da sauran Muhimman kayaki a dai dai wannan lokaci da sassan kasar yafada cikin kalubalen lafiya da Duniya ke fuskanta, Wanda tuni ya kawo nakaso wa cigaban Tattalin Arziki.

 

 

Shugaban ya Umarci dukkan hukumomi da abin ya shafa, da tsayayyun kungiyoyi masu gudanar da aiki, kan su samar da yanayi mai kyau, wa kamfanoni don su samu damar cigaba da Gudanar da aiki ta hanyar tabbatar da mihimman abubuwa da ga gwamnati da bukatun su kamar su ruwa, Man fetir, Iskar Gas, da wajibabbun aikin gina kasa, da saukaka Dokoki masu tsauri.

 

 

Ya jinjina wa Babban Bankin kasa CBN da bankunan Kasuwanci kan Gudumowa a bangaren Kudaden Chanji, da saukaka hanyoyin samar da bashi wa wa’an da ke bangaren kamfanin sarafa kayan masarufi.

 

 

Yayin bada karin tabbacin goyon baya ga kungiyar kamfanonin Sarrafa Kayan masa rufi, dakuma shirin dake akwai don magance kalubalen Annobar Cutar ga tattalin Arzikin Najeriya, Shugaban ya nemi bukatan daukan Dukkan wani mataki daya kamata don kare da kawo kula da lafiya dakuma bada kariya ga Ma’aikatan Kamfanoni.

 

 

Shugaba Buhari yayi kira ga dukkan Shugaban ni dake Daukacin fadin kasar nan, wanda suka hada da Shugabannin Addinai, Shugabannin Gargajiya, dasu kara azamar goyon bayan su ga Gwamnatocin Tarayya da Jiha kan shirye Shiryen fahimtar da Jama’a dake gudana kan bukatar nasu zauna a gida su nisanci Kansu da taron Jama’a, dakuma suja hankalin Al’umma kada firgita da wai-wai da masu yada jita-jita sukeyi kan cutar.

 

Shugaban ya kara jaddada kokarin aiyukan hadin gwaiwa daga dukkannin Al’ummar Najeriya zata kafa wani tarihi na daban na gudanar da binceke kan yaduwar cutar ta Covid-19, dakuma kara inganta wa’inda tuni suka kamu da cutar corona dakuma kare kasar.

Garba Shehu
Senior Special Assistant to the President
(Media & Publicity)
March 26, 2020

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *