Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar korona.
Mai magana da yawun ministan, Abubakar Sani ne ya tabbatar wa BBC da hakan.
A wani saƙo da ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa bayan ya ji alamun rashin lafiya, ya yanke shawarar yin gwaji wanda bayan gwajin aka tabbatar da ya kamu da cutar.
Ministan ya ce a halin yanzu lafiyarsa ƙalau amma yana jin ƙaiƙayi a maƙogwaronsa da kuma jin zazzaɓi da kuma mura mai majina.
Ministan ya kuma bayyana cewa tuni ya killace kansa inda yake ci gaba da shan magani.