Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa annobar cutar korona za ta ninka yawan mutanen da ke fuskantar masananciyar yunwa a duniya.
Hasashen hukumar ya ce an kara samun mutum miliyan 130 da ke fama da yunwa a duniya inda adadin ya karu zuwa mutum miliyan 265 a 2020 daga miliyan 135 a 2019 sakamakon tasirin annobar cutar korona ga tattalin arzikin duniya.
Gargadin na na WFP na zuwa a yayin da wasu alkalumma ke bayana matsalar abinci da ake fuskanta a sassan duniya.