fbpx
Friday, August 12
Shadow

Cutar Marburg mai yanayi da Ebola ta barke a kasar Ghana, inda har ta dauki rayuka biyu

Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da cewa a karin farko an samu mutane biyu dauke da cutar Marburg a yammacin nahiyar Afrika.

Inda hukumar ta bayyana cewa mutanen duk yan kasar Ghana ne kuma dukkansu cutar mai kama da Ebola ta kashe su bayan sun kami da ita.

Na farkon daya fara kamuwa da cutar dan shekara 26 kuma ya mutu baya kwana guda a asibiti, yayin da shima dai na biyun namijine dan shekara 51 kuma shi a ranar daya je aisbitu ya mutu.

Karanta wannan  Wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana

A karshe hukumar tace an killace mutane 90 da suka mu’amalanci wa’yanda cutar ta kashe a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.