Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa, An samu sabbin mutum 12 da suka harbu da cutar zazzabin Lassa a jihohi uku dake fadin Najeriya a makon farko na watan Fabrairun shekarar 2021.
Rahoton hukumar wanda ya gudana a tsakanin 1 ga watan Fabrairu zuwa 7 ga Fabrairu ya nuna cewa an samu sabbin wadanda suka harbu da cutar ne daga jahohin Edo, Ondo, da Taraba.
Jimillan mutane 66 ne suka kamu da cutar tun bayan shigowar wannan shekarar ta 2021.