fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Cututtukan da Auren Zumunci ka iya jawowa

Auren zumunci ko na dangi ba sabon abu ba ne tsakanin ƙabilu, inda wasu ƙabilun suke bayar da matuƙar muhimmanci a kansa domin inganta dangantakar da ke tsakaninsu.

Sai dai duk da auren zumunci da ake yi tsakanin ƴar wa da ɗan ƙane, da kuma makamantansu yana da fa’idoji ta ɓangaren zamantakewa da kuma ƙara danƙon zumunci, a kimiyance ta ɓangaren lafiya, likitoci sun ce yana da haɗari.

Dr Ibrahim Musa, masanin lafiyar jini a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano a arewacin Najeriya ya ce auren zumunci yana haifar da ƙarin yiwuwar samun cututtukan da ake gada daga iyaye.

Misali, kamar ciwon sikila wanda iyaye sukan kasance suna da nau’in wannan ciwon tare da su, idan aka ci gaba da auratayya ciwon zai ci gaba da yaɗuwa.

Sannan masanin ya ce akwai cututtuka da na gado wanɗanda auren zumunci ke haifarwa ba tare iyali sun sani ba.

Ƙwayar halittar dangi

Mujallar Lafiya ta The Lancet a 2013, ta ce ƙwayoyin halittar ma’aurata na iya shafar kowaɗanne ma’aurata, komai asalinsu ko ƙabilarsu.

Misali wadda ta auri ɗan uwanta da suke jini ɗaya za ta fi fuskantar matsala a ƴaƴan da za ta haifa.

Ko da yake a wani cikakken bayani da Hukumar Lafiya ta Ingila NHS ta yi game da matsalar ta ce ba a cika samun matsala ba a yawancin ƴaƴan da aka haifa ta hanyar auren zumunci, yawanci ana haihuwarsu ne da lafiya.

Amma ta ce auren zumunci kamar na ƴar wa da ɗan ƙane ko ƴaƴan wa da ƙanwa, ya fi haifar da matsala ga ƴaƴan da za su haifa da kashi uku zuwa shida, amma kuma matsalar ba mai yawa ba ce.

Ana samu matsala idan ma’auratan biyu sun gaji kwayoyin haliyyar da ke da matsala daga iyayensu.

Me ya sa ƙwayoyin halitta ke da muhimmanci ga dangi

Yan uwa daga dangi ɗaya suna da adadi mafi yawa tsakaninsu na ƙwayoyin halittarsu. Ƙwayoyin halittar kuma ginshiƙi ne da ke sarrafa jiki.

ƙwayoyin halittar ne ke daidaita launin ido da girmansa da girman ƙafafu da hannaye da sauransu.

Ana gadar abubuwa da dama daga iyaye, kamar yadda za mu iya gadar cututtuka da dama daga gare su, ta hanyar ƙwayar halittarsu.

Wannan zai iya shafar al’ummar da dama, amma ya fi yawa tsakanin dangin da ke auratayya tsakaninsu.

Haihuwar ƴaƴa da nakasa

NHS ta ce ana samun matsaloli na gado cikin kowace al’umma a duniya. Kuma al’ummar da ke yin auren zumunci sun fi yawan yaran da ke da matsaloli na gado.

A cewar NHS ƴan asalin asalin Pakistan a Birtaniya sun fi yin auren zumunci tsakaninsu, kuma tsakaninsu aka fi samun yaran da ake haihuwa da matsaloli na gado.

Dr Ibrahim ya ce tun da cutar tana cikin dangi kuma aka ci gaba da auratayya, ciwon zai ci gaba da yaɗuwa daga yayan da aka haifa,”

Sauran cututtukan gado da likita ya bayyana da ake samu ta hanyar auren zumunci sun hada da: Ciwon taɓin hankali da tawaya ta halitta.

A cewar likitan, bincike ya nuna ciwon na gado na haifar da yawan yin ɓari. Haka kuma yakan iya kara cutuka da ake gada kamar yawan zubar da jini.

“Ko a kwanakin baya an gano wasu ma’aurata a ƙaramar hukumar batsari ta jihar Katsina waɗanda suka kasance ƴaƴan maza zur, wato uban matar da uban mijin Hassan ne da Hussaini, sai suka haɗa ƴaƴansu aure.

“To ƴaƴan nasu ne suka dinga haifar ƴaƴa masu tawayar halitta, wato ba su da gurbin idanuwa, sannan wani hancinsa ya kwalmaɗe da sauransu.

“To wannan duk ba komai ya jawo ba sai abin da ake kira Fraser II syndrome wato wasu ƙwayoyin halitta na gado da suke da tawaya da ake samu daga jikin dukkan iyayen biyu da ke da alaƙa ta jini,” kamar yadda Dr Musa ya shaida wa BBC.

Kansar ido

Auren zumunci kan iya janyo wata nau’in cuta ta kansar ido, kamar yadda tsohuwar babbar jami’ar shirin taƙaita cutar kansa ta Najeriya, Dr. Ramatu Hassan ta bayyana a wata hira da BBC.

Cutar na fitowa ne a dai-dai inda ya kamata ido ya gani, sai a haifi yaro da ita a hankali a hankali tana ci gaba da girma, yayin da yaro ya kamata ya fara tafiya sai ya riƙa tuntube kamar yadda likitar ta bayyana.

Likitar ta ce auren zumunci ko na dangi da ake yi tsakanin mutane kan yi sanadin a haifi yaro mai irin wannan lalurar.

Kasashen da ke da yawan auren zumunci kamar arewacin Najeriya na da yawan cutar kamar yadda likitar ta bayyana.

“Irin wannan cuta ta kansar ido na samuwa ga jarirai tun suna cikin ciki, saboda gado ake yi yawanci, kuma yana faruwa a inda ake yawan yin auren dangi, don haka akwai yiwuwar idan aka ci gaba da auren dangi to kuwa za a ci gaba da samun cutar,” in ji ta.

Masana kiwon lafiya sun bayar da shawarwari cewa samun bayanan likita game da ƙwayar halitta abu ne mai muhimmanci ga dangi.

NHS ta ce Bayanan za su yi amfani ga duk wanda ke da matsala ta gado a danginsa ko kuma waɗanda ke da irin wannan damuwar.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.