fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Dumi: An damke dan sanda da laifin kisa a jihar Benue

Hukumar ‘yan sanda ta damke jami’inta sajan James Aondona da laifin kisa a karamar hukumar Katsina Ala dake jihar Benue.

Inda mai magana da yawun hukumar Sewuese Anene ta bayyana cewa an saka Aondona aiki ne a yankin ranar 26 ga watan yuni yayin da wannan lamarin ya faru.

Inda fada ya hada shi da wani mutun har ta kaiga ya aika shi barzahu, kuma gawar mutumun tana nan a asibitin karamar hukumar ta Katsina Ala.

Kwamihinan ‘yan sanda yayi tir da wannan laifin daya aikata kuma yace shi amintaccen jami’i bane sannan dole ya fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.