DA ƊUMIƊUMINSA: Ƴan Boko Haram Sun Sace Naira Miliyan 82 A Yayin Harin Da Suka Kai Gidan Yarin Kuje Dake Abuj
Daga Comr Nura Siniya
Shugaban Jami’an Kula Da Gidan Yari Na Ƙasa Halliru Nababa, yace ƴan Boko Haram sun sace naira Miliyan “82” a gidan yarin Kuje, a ya yin harin da suka kawo a daren Jiya Talata.
A cewar shi Ƴan Boko Haram 64 ne suka tsere daga cikin fursunonin fiye da 300 da suka gudu a harin da aka kai kan gidan yarin Kuje a Abuja.