DA ƊUMIƊUMINSA: Ana Tuhumar Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina A Jam’iyyar APC, Kuma Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Dr. Mustapha Inuwa, Da Sace Kudaden Tsaro Sama Da Naira Milyan 560.
Dan takarar Gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar APC kuma tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Dr. Mustapha Inuwa, ya sace kudaden tsaro har Naira milyan dari biyar da sittin 560 ta hanyar shirya bococin karya daga shekarar 2017 zuwa 2019 kamar yadda Jackson Ude, ya rubuta a shafinsa na Twitter.
A cikin tuhume tuhumen da ake ma tsohon sakataren gwamnatin Dr. Mustapha Inuwa aƙwai batun kuɗi Naira Miliyan 16 da suka yi ɓatan dabo a daren ranar 5 ga watan Junairu 2020. wanda albashin ma’aikatan wucin gadi na S-Power dake koyarwa a Makarantun firamare da sakandire.
Abin mamaki a wata fira da gidan rediyon Vision FM Katsina suka yi da tsohon sakataren gwamnatin yace baida kuɗi Naira dubu ɗari 250 ya mallaka a duniya sai gashi ya dira ofishin Jam’iyyar APC na ƙasa ya fitar da Zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan 50 ya sayi Fom na takarar kujerar Gwamna a jihar Katsina.