Wani matashi dan shekara 29 a jihar Maiguduri mai mayar da motocin man feyur zuwa na lantarki, Mustapha Gajibo ya bayyana dalilin dayasa ya bar makarantar Boko.
Mustapha yace ya bar makaranta ne domin ya cika burinsa na kere kere domin tun yana yaron wannan shine babban burinsa.
Inda yace kuma bai cire ran zama babban mai kudi ba kamar Bill Gates wanda shima saida ya bar makaranta kafin ya zama shahararren mai kudin Duniya.
A karshe Mustapha Majibo yace da ace bai bar makarnta ba da yanzu yana gararamba akan tituna yana neman aiki, kuma ya bar makarantar ne yayin daya ke aji karshe na kammala jami’ar Maiduguri