fbpx
Monday, June 27
Shadow

Da Dami Duminsa:Atiku zai zabi abokin takara ran talata, yayin da Tinubu ke shirin zabar musulmi

Hukumar zabe ta Najeriya, INEC ta bayyana cewa ba zata karawa jam’iyyu lokacin da zasu gabatar mata sunayen ‘yan takara da mataimakan su ba,

Wanda hakan yasa suma jam’iyyun suke kokarin ganin cewa sun gabatar mata dasu kafin wa’adin ya cika ranar 17 ga watan yuni watau juma’a mai zuwa.

Inda PDP ta shirya gudanar da gagarumin taro ranar talata da gwamnoni da sauran manyan jam’iyyar don zabarwa Atiku mataimakin da zai sa su lashe zaben 2023.

Yayin da jam’iyyar mulki ta APC ke shirin zabar musulmi a matsayin mataimakin Tinubu domin basu da wani kirista mai karfi sosai da ka iya sa jam’iyyar tayi nasarar lashe zaben 2023.

Karanta wannan  Buhari ya taya kakaakin majalisar wakilai munar cika shekara 60, yace ya cigaba da aiki tukuru kamar yadda yake yi

PDP na shirin zabar daya daga cikin Nyesom Wike ko kuma Udom yayin da APC ke shirin zabar LaLong, cikin musulmi kuma Badaru, El Rufa’i da Ganduje.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.