fbpx
Saturday, September 23
Shadow

DA DUMÍ – DUMÍ: A gobe Lahadi Jirgin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa birnin New York na ƙasar Amurka domin halartar babban taron Majalissar Dinkin Duniya (UN General Assembly) karo na 78 inda Shuwagabannin ƙasashen duniya sama da 150 ake sa ran za su halarta

DA DUMÍ – DUMÍ: A gobe Lahadi Jirgin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai shilla zuwa birnin New York na ƙasar Amurka domin halartar babban taron Majalissar Dinkin Duniya (UN General Assembly) karo na 78 inda Shuwagabannin ƙasashen duniya sama da 150 ake sa ran za su halarta.

Wannan shine karo na farko da shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron a matsayinsa na shugaban ƙasar Najeriya, kuma zai gabatar da Jawabinsa a rana ta farko ta gudanar da Taron.

Bayan gudanar da taron shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da Shuwagabannin ƙasashen Brazil, South Africa, da sauran Shuwagabannin ƙasashen duniya domin hadin gwiwa akan cigaban ƙasashen bakidaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *