fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Da Dumi Dumi: A yau ne Messi ya samu damar fara tattaunawa da wasu kungiyoyin dake harin siyan shi

A farko dai muna tayaku murnar shiga sabuwar shekara ta 2021 a yau ranar juma’a, yayin da kuma muke fatan samun saukin annobar korona wadda tasa yanzu wasan tamola yaja baya saboda hana yan kallo siga filaye.

Bayan wannan, muna farin cikin sanar daku cewa a yau rana ta farko ga watan janairu aka bude kasuwar yan wasan tamola domin baiwa kungiyoyi damar karawa tawagar su karfi yayin da ake tsaka da buga wasannin wannan kakar.

Bude kasuwar da aka yi ta baiwa gabadaya yan wasan da kwantirakin su zai kare a wanna kakar damar fara tattaunawa da wasu kungiyoyin dake harin siyan su, kuma babban dan wasan a cikin wa’yan da suka samu wannan damar shine kaftin din Barcelona Lionel Messi.

Har yanzu babu wata yarjejeniyar sabunta kwantirakin Messi a Barcelona bayan da suka hana shi canja sheka a shekarar data gabata, yayin da shima dan wasan ya bayyana cewa ba zai kammala yanke shawara ba har sai a karshen wannan kakar kuma zai cigaba da taimakawa Barcelona wurin samun nasara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.