Jam’iyyar All Progressives Congress APC, ta wargaza Kwamitin Gudanar ta Kasa.
An yanke hukuncin ne a taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar ranar alhamis.

Bashir Ahmad, mataimaki ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana a shafin sa na Twitter cewa, “Bayan shawarar Shugaba Muhammadu Buhari, Kwamitin Kasa (NWC) na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rushe.”
Mukaddashin shugaban APC, Victor Giadom ya nada gwamnan Yobe, Mai-Mala Buni a matsayin sabon shugaban kwamitin wucin gadi kuma nan take ministan shari’a, Abubakar Malami ya rantsar dashi.
Wannan mataki na nuni da cewa an gama da zancen Adams Oshiomhole.