Jam’iyyar APC ta daga ranar da zata kaddamar da Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
A ranar lahadin data gabata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin abokin takararsa.
Amma wasu gwamnonin Arewa na APC sun nuna bacin ransu akan hakan yayin da kuma yawancin kiristocin jam’iyyar suka sauya sheka.
Kuma jam’iyyar na shan suka wurin wasu ‘yan Najeriya cewa ta zabi Musulmi da Musulmi, amma duk da haka wasu da dama sun goyi bayan hakan.
Kuma a halin yanzu bata fadi ranar da zata kaddamar da Shettima ba.