Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta sanar da dage tantance daukacin masu neman tikitin yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa da aka kudurci farawa a ranar Litinin 23 ga wannan wata.
Sakataren watsa labaran jam’iyyar Mr. Felix Morka a cikin wata sanarwa, ya ce jam’iyyar za ta sanar da sabuwar ranar fara aiwatar da shirin.