Jam’iyyar mulki ta APC zata ganatarwa al’ummar Najeriya mataimakin dan takararta na shugaban kasa, wato Sanata Kashim Shettima.
Zata gabatar dashi ne a babban birnin tarayya Abuja ranar laraba 20 ga watan yuli a Shehu Musa Yar Adua da misalin karfe 11 na safe.
A kwanakin baya ne dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa.