fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Da Dumi Dumi: Atiku Abubakar ya dawo gida Najeriya domin halattar yakin neman zabe a jihar Osun

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya dawo gida Najeriya da safiyar ranar alhamis don halattar yakin neman zaben gwamnan jihar Osun.

Atiku ya bar al’amuransa da yaje gudanarwa a kasar Landan da Morocco da kuma Amurka bakidaya domin taya dan takarar gwamnan PDP na Osun, Adeleke yakin neman zabe yau alhamis.

Kuma wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar ta PDP sun sauka a jihar kamar su Bukola Saraki da gwamna Waziri Tambuwal domin tabbatar da cewa PDP ta lashe zaben a ranar asabar mai zuwa.

Karanta wannan  Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawa da fasinjojin jirgin kasa da suka samu 'yanci daga hannun 'yan bindiga

Dan takarar APC, Bola Ahmad Tinubu dana NNPP, Kwankwaso da kuma na jam’iyyar Labour Party Peter Obi duk sun halacci jihar sun gudabar da nasu yakin neman zaben.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.