fbpx
Monday, August 15
Shadow

Da Dumi Dumi: Bincike ya nuna cewa tilatawa tsohon shugaban alkalai Ibrahim Muhammad Tanko akayi yayi murbus

A jiya shugaba Muhammad Buhri ya rantsar da sabon shugaban alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola na wucin gadi a baban birnin tarayya Abuja.

Inda ya karbi mulkin daga hannun alkali Ibrahim Muhammad wanda yayi murabus saboda yace bashi da lafiya.

Amma rahotanni sun bayyan cewa tilastawa alkalin kotun kolin akayi yayi murabus, inda manyan alkalai 14 suka kai karansa fadar shugaban kasar, har sukace zasu daina aiki idan ba’a tsige shi ba kafin watan satumba.

Kuma sun kara da cewa baya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata kuma yana zuwa kasashen waje tare da iyalansa suna holewarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.