fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Da Dumi Dumi: Biyo bayan kuma batanci ga annabi a bauchi rikicin addini ya kaure

Daga Muhamma Kwairi Waziri

Wani Matashi mazaunin Garin warji ya shaida mana cewa, rikicin addinin ya kaure ne sanadiyyar batanci da wata Kirista tayiwa Fiyayyen Hallita a yammacin yau Juma’a.

Musulmai ma zauna garin sunyi kokarin wajen gano matar da tayi batanci ga Annabi domin dauka mataki, sai aka samu akasin haka matar ta gudu kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana.

Majiyar data bukaci aboye sunan ta tabbatar mana da cewa, ankona coci guda daya Sanadiyyar batanci da kirista tayi wa annabi a garin.

Karanta wannan  Hotuna: 'Yan Boko Haram masu tarin yawa sun tuba sun mika wuya

Sai dai daga karshe Kiristoci sun foto da Makamai manya man’yan- an’yan suna harbi agarin, zuwa yanzu haka sun harbi mutane 10, tare da jikkata mutane da dama a halin yanzu haka, kamar yadda daya daga cikin wanda aka harba ya tabbatar mana lamarin.

Daga karshe Jami’an tsaro sun isa garin domin kwantar da hankulan Al’ummar yankin.

Daga Alglfijir Hausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.