fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

DA DUMI-DUMI: Boko Haram sun kai hari Otal a Yobe, sun kashe baki, sun kona makaranta

Mayakan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram sun kai farmaki garin Geidam da ke jihar Yobe inda suka kashe baki 10 da suka je wata otal.

Sun kuma kona makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati, a garin. A cewar mazauna garin, ‘yan kungiyar sun kutsa cikin garin ne a daren Laraba ba tare da harbi ko daya ba.

An ce sun ajiye baburan nasu ne a wata unguwa da ke makwabtaka da su.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun shiga ta gabashin garin inda suka kona makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati Geidam, inda suka kashe mutum daya a harabar makarantar.

Karanta wannan  Allahu Akbar: Mutumin da yayi tattaki daga Afrika ta zuwa Makkah don aikin Hajji ya sauka bayan shekaru uku

A halin da ake ciki yanzu haka wasu mazauna garin na kauracewa garin domin gudun kada su makale kamar yadda ya faru a bara lokacin da maharan suka shafe kwanaki a cikin al’umma.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu damar jin ta bakin shugaban karamar hukumar Geidam Ali Kolo ba, amma mataimakinsa Musa Muhammed ya tabbatar da faruwar harin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.