fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Da Dumi Dumi: Bruno Fernandez yayi hatsari yayin da Man U ke shirin karawa da Liverpool ranar Talata

Tauraron dan wasan Manchester United, Bruno Fernandez yayi hatsari a motarsa ta Porsche da safiyar ranar litinin.

Amma ana san ran dan wasan mai shekaru 27 bai sami mummunan rauni ba kuma zai iya yin atisayi tare da abokan aikinsa anjima.

Manchester United na shirin karawa da abokan hamayyarta masu burin lashe kofin Firimiya, wato Liverpool da yammacin ranar Talata.

Kocin Unitef na wucin gadi, Ralf Rangnich zai yi jawabi anjima kuma ana sa ran zai yi bayanai akan dan wasan idan zai iya karawa da Liverpool gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.