Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci jami’an tsaro da su kubutar da duk mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na Kaduna da kuma sauran mutanen da ake garkuwa da su.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguno, shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis bayan taron majalisar tsaro ta kasa da shugaba Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Munguno ya ce shugaban kasar yana jin takaicin matsalar tsaro a kasar, don haka ya bukaci shugabannin tsaro su dauki matakin gaggawa.
Ya kuma yi kira da a karfafa tsaro a iyakokin kasar domin dakile rashin tsaro.
Da sabon umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro, ana sa ran nan ba da jimawa ba za a kubutar da wadanda aka sace.