Tauraron dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo wanda ya lashe kyautar zakaran dan wasan duniya sau biyar ba zai bugawa kungiyar wasanta da Liverpool ba yau.
Hakan ya faru ne biyo bayan mutuwar daya daga cikin yaransa da budurwarsa Geogina ta haifa masa jiya.
Inda kungiyar Manchester United ta bayyana cewa iyali na gaba da komai saboda haka ta bar dan wasan ya kasance tare da iyalansa.