Bulaliyar majalissa, Kalu ya jagoranci sanatocin APC guda 22 zuwa fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari yau ranar talata.
Inda suka cewa shugaban kasar sufa zasu sauya sheka saboda sakamakon zaben fidda gwanin da suka gani a yankunansu.
Amma shugaba Buhati ya basu hakuri yace tafiyar tasu babban kalubale ne ga jam’iyyar APC a halin yanzu.
Kuma sun amince sun fasa sauya shekar a cewar bulaliyar majalissar watau Kalu wanda ya jagorance su.