Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni, Dr Kayode Fayemi ya fito takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC.
Gwamnan ya fito takarar ne kwana daya ya bayyana ra’ayinsa na tsayawa takarar a APC, ya bayyana ra’ayin nasa ne a ranar laraba sai ya siya a ran Alhamis.
Amma jam’iyyar bata bayyana dalilin dayasa shi yayi hakan ba, inda tace ba laifi bane sayen Fom a sirrance.