Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayar da umurni a kulle gabadaya kasuwannnin dake Mada, Wunaka da Ruwan Bore a karamar hukumar Gusau, tare da masaurautar Yansoro tare da Yandoto dake karamar hukumar Tsafe.
Matawallen Zamfara ya hana tuka babura da sayar da man fetur a Mada, Wunaka, Ruwan Bore tare da masauratar Yandoto.
Inda gwamnan ya kara da cewa ya kullen kasuwannin ne da kuma hana tuka babura d sayar da mai saboda matsalar tsaron da ake fama dashi a yankunan.