Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya fadi zaben fidda gwani na shugaba kasa a jamiyyar PDP, zai gana da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a kasar Faransa.
Mai bawa gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu shawara ne ya bayyana hakan, wato Joe Igbokwe.
Gwamnan juhar Rivers din bayan ya fafi zaben fidda gwanin, Alhaji Atiku wanda ya lashe zaben yace zai zabe shi a matsayin abokin takararsa.
Amma daga bisani Atiku ya zabi gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa duk da cewa kwamitin PDP tace ya zabi Wike.