fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Da Dumi Dumi: Hukumar zabe ta INEC zata daina yiwa mutane rigistar katin zabe a wannan watan na Yuli

Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta bayyana ranar da zata daina yiwa mutanen Najeriya rigistar katin zabe ranar juma’a.

Inda kwamishinan dake magana da yawun hukumar, Fetus Okoye yace a karshen wannan watan ne zasu daina wato 31 kenan.

Hakan ya biyo baya ne bayan babbar korun tarayya tayi watsi da karan da hukumar kare hakkin bil’adama ta SERAP ta shugar kan hukumar zaben.

Inda ta bukaci INEC ta cigaba da yiwa mutane rigistar har sai zabe ya rage sauran kwanaki 90 zuwa zabe, amma kotun tace INEC ce keda wannan damar ta fadin lokacin da dake so ta kammala yiwa mutane rigistar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.