Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ci gaba da rijistar masu kada kuri’a (CVR) zai kare a ranar Alhamis 30 ga watan Yuni 202 a fadin kasar nan.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi a wurin taron gabatar da jama’a na shirin INEC na 2022-2026 Strategic Plan (SP) da 2023 Election Project Plan (EPP) a Abuja.
Shugaban ya tabbatar da cewa jaddawalin zaben 2023 bai canza ba, ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su hada kai da hukumar domin samun nasarar gudanar da zaben.