fbpx
Monday, August 3
Shadow

Da Dumi-Dumi: Kwamishinan Lafiya Na Jihar Ondo Dr. Wahab Adegbenro Ya Mutu Sakamon Cutar Korona

Majiya ta bayyana cewa Mista Adegbenro ya mutu ne a ranar Litinin din da ta gabata bayan da aka garzaya da shi wani asibiti a garin Owo bayan ya kamu da cutar Coronavirus.
“Kwamishinan ya mutu ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Owo kuma hakan ya jefa majalisar cikin rudani.
“Ya mutu ne gada cutar korona saboda ya kamu da kwayar cutar a baya kuma yana shan magunguna saboda kasancewar shi likita.”
Gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, a halin yanzu ya killace kansa bayan an gwada shi kuma sakamako ya nuna cewa yana da kwayar cutar a farkon makon nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *