Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zabi fasto Isaac Bishop Idahosa a matsayin abokin takararsa na zaben shekarar 2023.
Jam’iyyar NNPP ce ta bayyana hakan a shafinta na kafar sada zumunta ta Twitter ranar alhamis.
Wanda hakan ke kara tabbatar da cewa maganar maja tsakanin NNPP da Labour Party ta mutu domin Obi da Kwankwaso duk ba mai son zama mataimaki a cikin su.
Fasto Isaac Bishop Idahosa ya kasance daya daga cikin mayan fastocin jigar Edo kuma yayi iya rera wakar addinin kirista sosai, sannan kuma babbar hedikwatar cocinsa ta God First a Legas take.