Manchester United ta fara ganawa da Napoli don ta sayar mata da zakaran gwajinta dan Najeriya, watau Victor Osimhen.
Manchester na son sayen dan wasa gaba mai kyau ne don ya taimakawa Cristiano Ronaldo, wanda yaci kwallaye 18 cikin 57 data ci a kakar data gabata.
Kuma manyan kungiyoyin Ingila na neman dan Osimhen kamar irinsu Arsenal da Newcastle duk dai wasu rahotanni sun bayyana cewa baya son Newcastle din.