Manyan lauyoyin Najeriya guda uku sun maka ‘yan takarar shugaban kasa na jigajigan jam’iyyun Najeriya a kotu kan ta hana su tsayawa takarar shugaban kasa.
‘Yan takarar sun hada na Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC da Alhaji Abubakar Atiku na PDP sai kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour Party.
Inda lauyoyin suka bayyana cewa duk sun sabawa dokar kudin tsarin mulkin Najeriy saboda basu zabi abokan takararsu ba kafin su gudanar da zaben fidda gwani.