Wasu bata gari dake tada zaune tsaye sun kaiwa motar ‘yan jaridar dake rakiyar Tinubu kuma masu goya masa baya hari a jihar Legas.
A yau ranar lahadi tsohon gwamnan jihar Legas din ya koma maihaifar tasa bayan ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Kuma ‘yan ta’adan sun kaiwa motar ‘yan jaridar har ne a yankin Adeniji inda suka jefeta da duwatsu kuma sun rike makamai hannayensu hadda adduna.
Sun lalata motar sosai kuma sun fasa gilasanta.