Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, ya yi murabus daga mukamin kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar domin shiga takarar gwamna a 2023.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Alhaji Ibrahim Musa-Kalla ya fitar a Katsina.
A cewar sanarwar, murabus din ya yi daidai da shirye-shiryen mataimakin gwamnan na bayyana muradinsa na tsayawa takarar gwamna domin bin sashe na 84 (12) na dokar zabe ta 2022.
Musa-Kalla ya ce: “Alhaji Yakubu ya gode wa Allah da kuma Gwamna Aminu Masari da ya ba shi damar bayar da gudunmowa wajen dawo da aikin gona a jihar.