fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Da Dumi Dumi: Matasan APC sun nemi Tinubu ya canja Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

Matasan jam’iyyar APC sun bayyana cewa basu goyi bayan Kashim Shettima da Tinubu ya zaba ba a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa mai zuwa ba.

Inda suka bayyana cewa ya gaggauta canja shi ya zabi wani Kirista ko kuma fasto na arewacin Najeriya saboda basa goyon bayan Musulmi da Musulmi.

Shugaban kungiyar Abdullahi Saleh ne ya bayyanawa manema labarai hakan a babban birnin tarayya Abuja.

Dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa wato Kashim Shettima, wanda hakan yasa yake ta shan suka amma wasu na goyon bayan hakan.

Karanta wannan  Shugaba Buhari yace a lahire ne kadai babu matsar tsaro

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.