fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Da Dumi-Dumi: Mutane uku sun rasa rayukansu yayin wata arangama da akayi tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa

An bayar da rahoton kashe mutane uku a ranar asabar sakamakon wata arangamar da ta barke tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Shugaban karamar hukumar, Barkono Jaji-Adiyani wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce ya shaida jana’izar dukkan mamatan.
Hakanan, jami’in yada labarai na karamar hukumar, Sunusi Doro, ya kara da cewa fadan ya faru ne a lokacin da wani mazaunin unguwar Arin ya sami rauni yayin da wasu yan fulani suka tare shi a hanyar daji.
Ya ce lamarin ya haddasa rikici tsakanin al’ummomin manoma da makiyaya a yanzu.
Ya ce dukkan wadanda abin ya shafa mazauna garin Adiyani ne, inda Kanuri suka fi yawa.
Jami’in ya bayyana sunan mamatan, Muhammadu Baushe, Maigida Kolo kuma ya ce har yanzu ba a gano sunan mamacin na uku ba.
Kodayake, da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na yan sanda a jihar, SP Abdu Jinjiri ya ce har yanzu ba su samu ingantaccen rahoton daga sashen yan sanda a karamar hukumar Guri ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Sanata Ndume yace rayuwa a Maiduguri tafi kwanciyar hankali akan Abuja saboda matsalar tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published.