Sakamakon gwajin da akawa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan cutar Coronavirus/COVID-19 ya nuna cewa bashi dauke da cutar.
Babafemi Ojudu,me baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa ne ya bayyana haka ta shafinshi na Twitter inda yace sakamakon gwajin Osinbajo ya nuna cewa bashi da cutar.
A baya dai Rahotanni sun nuna cewa Osinbajo ya killace kansa saboda mu’amalar da yayi da Abba Kyari wanda ya kamu da cutar.