fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Da Dumi Dumi: Sarkin jihar Zamfara ya baiwa tubabben dan bindiga sarauta

Sarkin karamar hukumar Yandoto, Alhaji Aliyu Mafara ya baiwa tubabben dan bindiga, Adamu Aleiro sarauta a karamar hukumar.

Inda ya bashi sarauyar sarkin Fulanin kamar hukumar ta Yandoto wadda ta kasance daya daga cikin yankunan da yan bindigar suke kaiwa farmaki a jihar.

Kuma mai magana da yawun bakin fadar wato Lawali ya bayyanawa manema labarai cewa an baiwa Adamu sarautar ne saboda yanzu yana daya daga cikin masu son zaman lafiya a yankin.

Sannan wani labari me dadi shine manoma zasu fara zuwa gonakinsu ba tare da fargaba ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.