Sbugaban jam’iyyar PDP na jihar Sokoto kuma tsohon kansilan karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Jelani Danbuga ya koma jam’iyyar APC.
Malam Bashir Abubakar mataimakin Sanata Aliyu Wamako ne ya bayyanawa manema labarai wannan labarin a ranar litinin.
Inda Abubakar ya bayyana cewa Wamako, wanda ya kasance shugaban APC na jihar Sokoto yayi maraba da Danbuga a ranar asabar bayan ya sauya shekar.