Shugaban karamar hukumar Jada wadda ta kasance mahaifiyar Atiku dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar PDP, Hammantukur Yettusuri ya koma jam’iyyar NNPP.
Ya koma jam’iyyar ta NNPP a ofishinta dake babban birnin jihar Adamawa wato Yola inda shima ya koma bayan Kwankwasiyya.
Kuma ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda akwai lauje cikin nadi sai yasa ya koma bin bayan jam’iyyar mai son gaskiya ta NNPP.