Motocin bas din sun ce an yi awon gaba da su ne kan hanyar Degema/Buguma/Abonnema da ke kan titin Gabas/Yamma a kan hanyar zuwa Kalabari a karamar hukumar Degema, Asaritoru da Akukutoru daga Fatakwal.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba amma mazauna yankin sun ce abin ya haifar da tashin hankali a yankin.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a san inda fasinjojin da motocin bas din suke ba.
Cikakkun bayanai na nan tafe anjima…