fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Da Dumi Dumi: ‘Yan bindiga sun kafa tasu gwamnatin a karamar hukumar Mada dake jihar Zamfara

‘Yan bindigar dake hari karamar hukumar Mada dake jihar Zamfara sun mamayeta bakidaya sun mafa tasu gwamnatin, cewar mazauna yankin.

Wanda hakan yasa yawancin mazauna karamar hukumar suka tsere suka bar gidanjensu saboda harin da ‘yan bindiga ke kai masu kamari sosai.

Domin yanzu ‘yan ta’addan sunfi karfin hukumar yayin da su kuma mazauna yankin suka zamo ‘yan gudun hijira bayan da suka tare akan hanyar Mada zuwa Kotorkoshi.

Inda wani mazaunin yankin Malam Ibrahim ya bayyana cewa sun dade basu yi wanka ba soboda ‘yan bindiga sun kore su a gidajensu, kuma yanzu haka bai san inda matarsa da yaransa suke ba.

Amma gwamnatin jihar ta kulle gabadaya kasuwannin Mada kuma ta hana tuka babura da sayar da man fetur a yankin.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *