‘Yan bindiga sun kashe babban jami’in dan sanda, ASP Chris Josiah a jihar Patakwala ranar talata da misalin karfe tara da dare yayin da yake dawowa daga wurin aikinsa.
Mai magana da yawun hukumar ta jihar, Grace ce ta bayyana hakan, kuma tace ba zasu lamince kashe-kashen jami’ansu a jihar Patakwal ba saboda haka dole a nemo mutanen da suka aikata wannan bannar.
Inda tace hukumar ta saka jami’ai da dama farautar ‘yan ta’addan da suka aikata wannan laifin domin a gaggauta hukunta su.