Wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.
Ofishin da ke hedikwatar majalisar a Ogurute ya kone kurmus a daren Lahadi kuma ginin da abin ya shafa ya kone gaba daya.
An tattaro cewa hukumar kashe gobara ta jihar da ke da ofishi a Ogurute ta kasa shiga domin kashe gobarar saboda fargabar sake kai hare-hare har sai da aka samar da jami’an tsaro, yayin da kafin isowarsu ofishin ya kone kurmus.
Cikakken rahoto yana nan tafe….