fbpx
Monday, June 27
Shadow

DA DUMI-DUMI: Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar Sanatan APC a Kano ta Tsakiya

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar Sanata a jihar Kano ta tsakiya na APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da A. A Zaura.

Rahotanni sun bayyana cewa, an sace mahaifiyar dan siyasar, Hajiya Laure Mai Kunu a gidanta da ke unguwar Rangaza a kauyen Zaura a karamar hukumar Kumbotso a cikin birnin Kano a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, 2022.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na safe.

Karanta wannan  Hukumar NAFDAC ta haramta yin amfani da wani man kai da ake sarrafawa a Nahiyar Turai

SP Kiyawa ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kaddamar da tawaga ta musamman domin ceto matar tare da cafke Yan bindigar..

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.