Chris Oghojafor ya kasance dalibin shekarar karshe a kwalejin kimiyya da fasaha ta Delta, watau Abraka dake karamar hukumar Ethiope a jihar.
Sunyi garkuwa da shi ne a ranar juma’a a karamar hukumar ta Ethiope, inda suka kira ‘yan uwanshi suka bukaci a basu naira miliyan 50 kudin fansa.
Amma daga bisani sun sasanta a naira miliyan uku, a cewar mahaifin shi Oghojafor.