Taohon hadimin shugaban Muhammadu Buhar, Bashir Ahmad ya gargadi ‘yan takarar shugaban kasa cewa Peter Obi na mamaye manyan jihohin arewa.
Inda yace ya kai ziyara Kano a kwanakin nan kuma ko ina labarin Peter Obi suke ba wanda ke yin magana akan sauran ‘yan takarar shugaban kasan Najeriya.
Kuma amininsa ya fada masa cewa a jihar shugaba Buhari ma hakane watau Katsina suma Peter Obi suke so.
Saboda haka zai lashe kaso 75 zuwa 80 a jihohin guda biyu.